Hukumar kwastam ta yi nasarar cafke harsasai dubu dari da tamanin da tara da aka yi yunkurin shiga da su daga kasar Jamhuriyar Benin. Kwanturolan hukumar mai kula da jihohin Kwara, Kogi da kuma jihar Neja Mista Benjamin Binga ya ce sun kama harsasan ne a bakin iyakar Najeriya da kasar ta Jamhuriyar Benin da ke garin Babanna a Jihar Neja.
Kwanturolan ya bayyana cewa da sanyin safiyar Lahadin da ya gabata ne jami'an hukumar suka sanar da shi cewa sun cafke wata babbar mota kirar a-kori-kura inda ya basu umarnin kawo motar ofishinsu domin a bincika.
" Bayan bincike ne muka gano motar na dauke da harsasai na kusan dubu dari da tamanin da tara."
A yanzu dai haka jami'an kwastam na rike da mutane biyu da aka kama da harsasan. Dan Najeriya guda dan asalin jihar Anambra mai suna Martins Anokwara wanda shi ne mai kayan. Sai direban motar dan asalin kasar Jamhuriyar Benin, mai suna Bakari Dauda.
Wannan lamarin abin tayar da hankali ne ga 'yan Najeriya musamman ganin yadda halin tsaro ya kasance.
" Ga zaben 2019, ga matsalar 'yan Biafra, ga rikicin addini da na makiyaya da manoma, to ka ga wadannan abubuwa a ce kuma a na samun mutane na shigowa da harsasai to ba karamin abin tashin hankali ba ne," inji wani Aliyu Muhammad Lawal.
Duk da cewa ba a bari manema labarai sun dauki muryar wadanda aka kama ba, shi mai kayan Martins cewa yayi zai kai harsashen ne garin Onitsha ta jihar Anambra domin sayarwa maharba.