Baya ga matsalar Boko Haram da,garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kuma matsalar yan fashi da makami da kan tare hanya, wata matsalar kuma dake addabar jama’a a jihohin Adamawa da Taraba ita ce, ta yan Shila da kuma Yan Base.
Su dai ’Yan Shila, da akasarin su matasa ne da kananan yara, wadanda suka kware ne wajen yankan aljihu, da kwace wayar salula, da kuma yiwa mata fyade . Kuma wadannan matasa ’yan kimanin shekara goma sha biyar zuwa ashirin suna amfani da baburan hawa irin na Keke Napep ko kuma a daidaita sahu domin yi wa jama’a kwace , musamman idan yamma ta gabato ko kuma da dare.
To amma a wani yanayi na ba saban ba, wasu daga cikin wadannan gungun yan Shila sama da 34 sun mika wuya, sun tuba tare da mika makamansu ga sarakuna iyayen al’umma.
Daya daga coikin ‘yan shilan y ace da dare sukan tare mutum su ce ya kawo wayarsa idan kuma bai basu ba sais u yi mashi duka su kwace wayar. Yana cewa yanzu sun yi nadama sun tuba
Mudi wanda aka boye sunansa na ainihi,shi ya jagoranci yan shilan da suka tuba. Ya bukaci sauran matasa dake cikin irin wadannan kungiyoyin daba da su tuba, kana kuma a taya su da addu’a. Ya ce yana jawo hankalin sauran su tuba su kuma tabbata ba’a sake samun su da irin wannan aika aikar ba
An dai samu nasarar sauya tunaninsu ne ta hanyar hada hannu da shugabanin al’umma. Alhaji Muhammad Baba Sarkin yakin Jimeta na cikin wadanda ke tsayin daka kan wannan yunkuri ayanzu. Ya ce babu yaron da zasu kira da ba zai zo ba saboda har dakin uwarsa zasu bishi su daukeshi. Fatansu shi ne duk sauran zasu tuba gaba daya.
Da yake jawabi wajen wankan tsarkin da aka yiwa wadanda suka tuban Dan Isan Adamawa kuma Hakimin Jimeta Alhaji Muhammad Inuwa Baba Paris yace dole iyaye su tashi tsaye. Y ace idan aka ga yadda yara maza su keyi da yara mata abun tausayi ne. Ya bada misalign wata ‘yar shekara 13 da suka kai daji suka yi mata fyade har ta rasu suka binneta a wurin.
Tuni dai masarautar Adamawa ta kaddamar da wani shiri na yaki da fitsara na yan shila da kuma yan yawon tazubar,inda aka umarci hakimai da su tashi tsaye domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz
Facebook Forum