Ana Binciken Tsohon Shugaban Kasar Misira Mohamed Morsi

Mohammed Morsi Tsohon shugaban kasar Masar

Hukumomi a kasar Misira suna binciken Mohamed Morsi bisa zargin leken asiri da gunguntar da tattalin arzikin kasar
Masu shigar da kara na kasar Misira sun kaddamar da bincike jiya asabar kan shugaban kasar na farko da aka zaba karkashin tsarin damokaradiya.

Masu shigar da karar sun ce sun sami korafi a kan hambararren shugaban kasar Mohamed Morsi da wadansu kusoshin kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi da suka hada da shugabanta, Mohammed Badie.

An yiwa Mr. Morsi daurin talala a wani wurin da ba a bayyana ba tunda aka sauke shi daga karagar mulki ranar 3 ga watan Yuli, sai dai har yanzu ba a tukume shi da wani laifi ba.

Masu shigar da karar basu bayyana wadanda suka shigar da korafin ba, da ya hada da leken asiri da kuma raunata tattalin arzikin kasar.

A halin da ake ciki kuma, magoya bayan hambararren shugaban kasar sun ci gaba da zaman dirshe a dandalin Rabaa el-Adawi jiya asabar, suka kuma lashi takobin ci gaba da zanga zanga har sai an maida Mr. Morsi daga karagar mulki.

Masu zanga zangar sun yi tururuwa a dandalin duk da kazamin zafi da ake fama da kuma azumi da suke ciki.