Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Hambare Shugaba Muhammad Morsi Na Misra


Dubban masu zanga-zangar kin Shugaba Muhammad Morsi na Masar kenan a Dandalin Tahrir da ke birnin Alkhahira
Dubban masu zanga-zangar kin Shugaba Muhammad Morsi na Masar kenan a Dandalin Tahrir da ke birnin Alkhahira

Sojojin Misra sun hambarar da shugaban kasar na farko da aka taba zaba ta hanyar dimokuradiyya.

Sojojin Misra sun hambarar da shugaban kasar na farko da aka taba zaba ta hanyar dimokuradiyya, suka nada wani shugaban kasa na rikon kwarya a bayan da aka gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati.

A cikin wani jawabin da yayi ta cikin talabijin jiya laraba da maraice, babban hafsan sojojin kasar, Abdul Fatah Khalil al-Sisi, yace an dakatar da aiki da tsarin mulkin Masar, an kuma nada shugaban kotun koli ta tsarin mulki a zaman shugaban kasa na riko. Sisi yace sojojin su na amsa kiran al’ummar Masar ne a bayan gagarumar zanga-zangar ‘yan adawa cewa lallai shugaba Mohammed Morsi yayi murabus.

A martanin da ya maida ta shafinsa na Twitter a kan Intanet, Morsi yace matakin da sojojin suka dauka, juyin mulki ne kawai. Yayi kira ga dukkan al’ummar Masar da su ki yarda da wannan mataki na sojojin, amma yace su yi komai cikin lumana. Ba a san inda hambararren shugaban yake a yanzu ba.
Sabon shugaban riko na Masar shi ne Adly mansour, mai shekaru 68 da haihuwa,

kuma babban jojin kotun koli ta tsarin mulki. Yau alhamis za a rantsar da shi.
Rahotanni da dama sun ce an kashe mutane akalla 5 a fadan da aka gwabza a tsakanin magoya baya da masu adawa da Mohammed morsi a bayan da sojojin suka ce sun hambarar da shi. Dubban masu zanga-zanga na dukkan bangarorin biyu sun ci gaba da zama a kan titunan birnin al-Qahira har ya zuwa cikin daren laraba.

Rundunar sojojin Misra, ta girka zaratan dakarunta da motoci masu sulke a biranen dake fadin kasar domin hana barkewar tashin hankali. An girka dakarun tsaro a muhimman wurare da cibiyoyi na birnin al-Qahira, sannan kuma sun killace inda magoya bayan Morsi suke gudanar da gangami a wani yunkurin hana yaduwar wannan gangami nasu.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yayi kiran da a kwantar da hankula a kuma kare muhimman hakkokin al’umma a Masar, ciki har da ‘yancin fadin albarkacin baki da na yin taro.
XS
SM
MD
LG