An Zargi Jami'an Tsaro da Ruruta Wutar Rikici

Alumomin Birom da Fulani, na jihar Filato, masauna jihar Adamawa, sun nuna takaici da rashin jin dadinsu dangane da tashe tashen hankula da yankin ke fama dasu, masamman wadanda suka barke a 'yan kwanakin nan.

Sakamakon haka ya sa suka yunkura wajen bada tasu gudunmawa domin maido da zaman lafiya, a tsakanin alumar Birom, da Fulani.

shugaban alumar Birom, masauna Jihar Adamawa, Malam Yakubu Dawad, da jami'in tuntubar jama'a, na kungiyar Miyetti Allah na kasa Malam Sanusi Bara, sun ce baya ga tuntubar juna da zaman tattaunawa da suke yi daga lokaci zuwa lokaci suna baiwa alumominsu dake saune a gida Filatoi, shawarwari ta yadda zasu zauna lafiya da juna.

Shugabanin biyu, sun zargi jami'an tsaro da nuna rashin adalci da son rai a duk lokacin da aka samu barkewar rikici a yankin jihar Filato, alamarin da suka ce ya na ruruta wutar rikici wanda yaki ci yaki ciyewa kuma yana maida hannin agogo baya a kokarin da ake yi na ganin cewa an kawo zaman lafiya a yakin Filato.