Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sergio Ramos Zama Daram a Real Madrid


 Sergio Ramos
Sergio Ramos

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta tabbatar da rahotannin cewa kyaftin din ta, Sergio Ramos, babu inda za shi a bana, ko a shekara mai zuwa ma, domin ya yarda zai rattaba hannu kan sabuwar kwantaraki ta tsawon shekaru 5.

An sha rade-radin cewa Manchester United ta ware kudi maid an Karen yawa zata sayi Ramos a bayan da aka ce wai an samu rashin jituwa a tsakaninsa da shugaban kungiyar Real Madrid, Florentino Perez. Amma a yau litinin, Real Madrid, daya daga cikin manyan kungiyoyin tamaula na kasar Spain, ta ce a yau din, Ramos zai rattaba hannu kan wannan sabuwar kwantaraki a filin wasansu da aka fi sani da sunan Santiago Bernabeu.

Real ta kira wani taron manema labarai nan gaba a yau litinin tare da Ramos, sannan ta tabbatar ta cikin shafinta na Twitter cewa zai rattaba hannu kan kwantarakin da zata sanya shi zama a Real har zuwa shekarar 2020.

Manajan Manchester United, Louis Van Gaal, ya kosa a kan ya sayi Ramos, inda har aka ce ya ma shirya ba ita kungiyar Real mai tsaron gida David de Gea a zaman wani bangare na kudin sayen Ramos. Shi kansa Ramos an ce ya fadawa Real a lokacin da aka fara saye da sayar da ‘yan wasa cewa yana son komawa Ingila, amma sai shugaban kulob din Perez yace atafau.

XS
SM
MD
LG