An yiwa Sudan da Sudan ta kudu kashedin aza musu takunkumi

Wani sojan Sudan yake sintiri, bayan arangamar da aka yi tsakanin sojojin Sudan da Sudan ta kudu a garin Talodi.

Amirka ta gabatar da daftarin wani kuduri ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dake yiwa kasashen Sudan da Sudan ta kudu kashedin cewa su magance rikice rikicen dake tsakaninsu.

Amirka ta gabatarwa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya datfarin wani kudurin dake yiwa kasashen Sudan da Sudan ta kudu kashedin cewa, za'a azawa musu takunkunmi idan basu kaddamar da shirin samun zaman lafiya na kungiyar kasashen Afrika domin kawo karshen fafatawa akan iyakarsu ba.

Kungiyar kasashen Afrika tana son kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya goyi bayan shirin samun zaman lafiya data amince dashi a farkon wannan makon. Shirin ya tanadi kasashen biyu su magance rikice rikicensu akan albarka mai da batutuwan kan iyakokinsu da wasu batutuwa cikin kwanaki casa'in.

Jakadiyar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice, tace an shirya kwamitin sulhu ya fara tattauna kudurin da Amirka ke marawa baya a ranar Alhamis domin a baiwa shawarar da kungiyar kasashen Afrika ta gabatar goyon baya cikin sauri.

Copi na daftarin da yan jarida suka gani yace kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya mai wakilai goma sha biyar zaiyi nazarin kaddamar da bukatun kungiyar kasashen Afrika kuma kwamitin zai iya daukan wasu matakai idan bukatar haka ta taso.