Wata majiya daga rundunar sojojin Sudan ta fadawa Muryar Amurka cewa an yiwa shugaban kasa Omar al-Bashir daurin talala, yayin da sojoji da shugabannin siyasa ke tattauna yadda za a yi sauyin gwamnati.
Rahotanni sun ce hukumomi sun rufe babbar tasahar jiragen saman kasar, sun kuma kama jami’ai da shugabannin sojoji da aka yi imanin su na bayan Omar al-Bashir.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar da rahotan da ke cewa sojojin Sudan sun afkawa jam’iyyar al-Bashir ta NCP.
Ya zuwa yanzu dai mai magana da yawun jam’iyyar bai amsawa Muryar Amurka ba akan batun.
Dubban masu zanga-zanga sun fito kan tituna a birnin Khartoum su na murna, suna fadin cewa suna goyon bayan sojoji.
Fatima, na daga cikin masu zanga-znagar kuma ta ajiye ‘ya ‘yanta kan babban titi yayin da motoci ke ta busa kararwar mota domin nuna goyon bayan su.
Fatima ta ce su ba beraye ba ne, kamar yadda gwamnatin ta kwatanta masu zanga-zangar. ta kara da cewa "su zakuna ne." kuma ba zasu bar kan titun ba har sai sun ji sanarwar da jami’an sojoji za su yi.
Tabbacin cewa an sauke shugaban mai shekaru 75, na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da gidan Talabijin mallakar gwamnatin Sudan ya sanar da cewa sojoji za su yi wata muhimmiyar sanarwa.
ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5