Kwanaki 6 na yin ban kwana da gawar Jimmy Carter sun kare a yau Alhamis inda shugaban Amurka na 39 ya samu jana’izar ban girma a babban majami’ar kasar gabanin mayar da gawar tasa zuwa mahaifarsa ta Plains da ke Georgia, domin birnewa a gefen matarsa, Rosalynn.
Taron addu’o’in ya kawo karshen bajen kolin gawarsa a Majalisar Dokokin kasar, inda a jiya Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris ta jagoranci bikin bayyana yabo ga mamacin.
Shugabannin Amurka 5 da ke raye ne suka halarci jerin gwanon rakiyar gawar shugaban Amurka mafi dadewa a raye, cikinsu kuwa harda zababben shugaban kasa Donald Trump.
Bayan kammala taron addu’o’i a babban cocin kasar, za a mayar da gawar Carter zuwa mahaifarsa ta Plains, dan karamin garin da ya fara tare da kare rayuwarsa ta shekaru 100.
Za a gudanar da wata kebabbiyar jana’izar a majami’ar Baptist ta Maranatha, inda ya koyar a makarantar Lahadi bayan da shekarunsa sun zarta 90, gabanin a birne shi a gefen mai dakinsa Rosalynn, da suka shafe shekaru 77 a tare.