A Jamhuriyar Nijar, ana ci gaba da dakon sakamakon zaben da aka gudanar a jiya Laraba 31 ga watan Yuli da nufin saka tsari akan maganar kare hakkin ma’aikata.
Hakan tna faruwa ne bayan la’akari da yadda yawaitar kafuwar kungiyoyin kwadago a ‘yan shekarun nan ke haddasa cikas ga dukkan wani shirin sulhu a tsakanin gwamnatin kasar da shugabannin kungiyoyin kwadago, al'amarin da ke ragewa kasar mutunci a idon hukumar kwadago ta duniya.
Ma’aikata 185.909 ne suka yi rajistar wannan zabe domin raba gardama a tsakanin kungiyoyin kwadago kimanin 12 da ake da su a wannan kasa.
Gwamnatin Nijar ce ta shirya wannan zabe da nufin tantance kungiyoyin da za su tunkare ta da bukatun ma’aikata anan gaba, matakin da ake gani zai karawa kasar matsayi a idon hukumar kwadago ta duniya wato BIT, wadda ke fatan a samun hadin kai a tsakanin ma’aikata cikin kowane hali.
A yanzu haka kungiyoyin kawadago sun dukufa ga tattara sakamakon da ke zuwa masu daga sassan kasar.
Mataimakin sakataren kungiyar CDTN Malan Ibro Kane, ya ce akwai alamun haske a wannan shirin.
Kungiyar USTN wacce ta yi dawainiyar kwadagon ma’aikata a zamanin da al’umar Nijar ke gwagwarmayar kawo karshen mulkin danniyar da kasar ke karkashinsa a 1990, na daga cikin kungiyoyin da suka fafata a wannan zabe da ke matsayin na farko da ake shirya makamancinsa a tarihin Nijar.
A cewar magatakardanta, Mahaman Zaman Allah, suna da kwarin gwiwar samun kyaukyawan sakamako koda yake sun gano alamun murdiya.
Sai dai ministan kwadago, Ben Omar Mohamed, ya bayyana cewa komai zai gudana cikin haske, saboda haka gwamnati za ta yi na’am da duk kungiyar da ta yi nasara a wannan zabe.
Hukumar zabe ta CONEP ana ta bangare ta kafa sansanin musamman a ofishinta dake birnin Yamai, inda take tattara takardun sakamakon da ke shigo ta daga yankunan karkara, lokacin da wasun ke bayarda alkalumman ta hanyar waya.
A farkon watan nan na Augusta ne ake sa ran bayyana sakamako, kuma a kan ka’idar wannan zabe dukkan kungiyar kwadagon da ta gaza samun kashi 5 daga cikin 100 na kuri’un da aka kada, ta fadi warwas.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5