An Yi Zaben Kananan Hukumomi Lami Lafiya a Jihar Nassarawa

Keffi Nassarawa

Sai dai kuma wani direba ya gudu da kayayyakin zabe na wata mazabar da aka ba shi alhakin kai wa, kuma jami'an tsaro na nemansa.
An gudanar da zaben kananan hukumomi cikin kwanciyar hankali, duk da korafin rashin isar kayan aiki wasu mazabun, a Jihar Nassarawa.

Wasu masu jefa kuri'ar sun shaidawa wakiliyar Sashen Hausa cewa an yi zaben cikin lumana, inda jama'a suka ji kiran da hukuma ta yi na a gudanar da zaben ba tare da tashin hankali ba. Wani mai kada kuri'ar ma yace an yi shekaru masu yawan gaske ba a gudanar da zaben da aka yi shi cikin kwanciyar hankali kamar wannan ba.

Sai dai kuma a karamar hukumar Nassarawa, Sanata Walid Jibrin, sakataren kwamitin amintattun jam'iyyar PDP, yayi kukar cewa har zuwa karfe 2 na rana babu kayan aiki, kuma ba a fara zaben ba. Shi ma sanata Abubakar Sodangi na jam'iyyar PDP yayi irin wannan korafi tare da zargin cewa ana neman juya sakamakon zaben ne, amma sune masu nasara.

Kwamishinar hukumar zaben jihar Nassarawa, Maryam Musa, ta ce lallai an samu cikas a Nassarawa-Toto, inda wani direban da aka ba shi kaya daga hedkwatar karamar hukuma zuwa ofishin 'yan sanda, ya arce da su, ba a san inda ya shiga ko manufarsa ba. Ta ce jami'an tsaro sun sani, kuma su kansu wakilan dukkan jam'iyyun sun samu cikakken bayanin wannan lamarin.

Gwamna Umaru Tanko Al-Makura, yace shekaru 6 ke nan ba a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar ba, abinda ya sa ke nan ya dage a kan lallai sai an yi zabe domin tabbatar da cewa dimokuradiyya ta samu tun daga tushe.

Your browser doesn’t support HTML5

An Yi Zaben Kananan Hukumomi Cikin Kwanciyar Hankali a Jihar Nassarawa - 4'07'