Wadanda suka halarce taron sun bayyana abubuwan dake ci masu tuwo a kwarya.
WASHINGTON DC —
Kungiyoyin manoma da makiyaya, da sarakunan gargajiya tare da masana dokoki akan harkokin noma da kiwo sun yi wani taro na share fagen babban taron da za su yi a watan Decemba mai zuwa, akan kaddamar da kundin da zai kayyade al'amaran noma da kiwo a cewar Madam Hima Fatimatu, wata ‘yar kungiyar ‘yan karkara a Nijar.
Wani kwamiti ne da ofishin gidan gonar kasar ya kafa ya shirya taron don yin tsare-tsaren babban taron da zai hada manoma da makiyaya don samo bakin zaren matsalolinsu.
Oroji Bugau na haddaiyar kungiyar makiyaya na Rufen daga Maradi, ya ce babar matsalar ta samo asali ne daga rashin aiki da dokoki.
Ga karin bayani cikin sauti daga wakiliyar sashen hausa Tamar Abari.
Your browser doesn’t support HTML5