Shirin karbar haraji akan wasu ababen da a can da ba su da haraji da yinkurin farfado da wasu dokokin da gwamnatocin da suka shude suka jingine saboda wasu dalilai, shi ke kara harzuka jama’a da wasu kungiyoyin dake fafutikar kare hakkokin jama’a kamar MPCR ta Nuhu Muhammadu Arzika, da suka fara kalubalantar wadannna matakan da suke gani za su iya jefa jama’a a cikin kuncin rayuwa.
Domin haska fitila akan sabuwar dokar harajin dake shan suka daga rukunonin al’umma, missali karbar haraji daga dukiyar da mamaci ya barwa magadansa, ministan kudi Hassoumi Massaoudou ya hallara a zauren majalissa a jiya Laraba, to amma dan majalisar dokoki na bangaren adawa, Sumana Sanda ya ce basu gamsu da bayanin da aka yi masu ba.
Sai dai shugaban kwamitin kula da sha’anin kudi a majalisar dokokin kasar, honorable Adamu Namata, ya ce ba za su amince da abinda zai jefa jama’a ko kasar cikin wani mummunan hali ba, don haka a shirye suke su saurari ra’ayoyin jama’a da na kungiyoyin kare hakkokin bil’adama.
Kungiyoyin farafen hula dake adawa da wannan sabuwar dokar ta haraji, sun kudiri aniyar gudanar da zanga-zanga domin tilastawa gwamnati ta canza ra’ayi. Matakin da masu rinjaye a majalissar ke ganin rashin cancantarsa.
Wakilin muryar Amurka Sule Mumuni Barma na da Karin bayani a cikin sauti.
Facebook Forum