Shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya tsallake rijiya da baya, bayan da aka kai hari na tsawon sa’a guda a gidansa, wanda ya sa gidan ya huhhuje da harbin bindigogin da wasu da ba a san ko wadannene ba, su ka kai harin da safiyar yau Talata.
An bayar da rahoton mutuwar mutun guda a wannan harin. Kafar yada labarai ta Associated Press t ace wanda abin ya rutsa das hi din wani daga cikin dogarawan Fadar shugaban kasar ne.
Mr. Conde, wanda bai sami rauni ba a harin, daga bisani ya yi jawabi ga kasar inda ya bukaci da a kwantar da hankali.
Wannan mummunan harin ya kawo karshe ne bayan da sojoji su ka mamaye unguwar Kaporo Rails. Wani shaidan gani da ido ya gaya wa Muryar Amurka cewa sojoji sun killace wuraren da ke kewaye da gidan.
Kasar Guinea dai ta yi zaben ta mai inganci a karo na farko a bara. Wannan kasa mai arzikin ma’adanai na da tarihin saurin juyin mulki.