Shahararen dan wasan gaba nan kuma dan wasan da yafi kowani dan wasan kwallon kafa tsada a duniya Neymar, wanda yanzu haka yake taka leda a kungiyar Paris Saint-Germain, akan kudi yuro miliyan €222, yace zaiyi duk abinda zai iya yi don ganin ya kar kato ra'ayin abokin wasansa na kasar Brazil Philippe Coutinho, ya dawo kungiyarsu ta PSG daga kungiyarsa ta Liverpool, a memakon Barcelona.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tace tana hangen cewar mai horar da ‘yan wasanta José Mourinho zai iya komawa kungiyar Paris Saint- Germain, a karshen kakar wasan bana.
Shi kuwa Jose Mourinho, yana ta kokarin ganin ya dauko danwasan baya ne na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, mai suna Samuel Umtiti mai shekaru 23, da haihuwa zuwa kungiyar Manchester United a watan Janairu 2018.
Real Madrid, tace dan wasan gaba na kungiyar Tottenham, mai suna Harry Kane, mai shekaru 24, a duniya shine farkon zabinta wanda take ganin zai maye gurbin Karim Benzema.
Kungiyar Arsenal, ta bukaci fam miliyan £30 a tashin farko daga Manchester United, in har tana bukatar Mesut Ozil, wanda kwangilarsa zai kare da Arsenal, a karshen kakar wasan bana.
Shi kuwa Sergio Aguero na Manchester City ya bayyana cewar a shekara 2019, zai koma tsohowar kungiyarsa da yafara kwallo tun yana dan yaro mai suna Independiente in Buenos Aires.
Ita kuwa Manchester City tace zata kara tsawaita zaman dan wasanta na gaba mai suna Gabriel Jesus, mai shekaru 20, da haihuwa inda tayi alkawarin biyansa fam dubu £100 duk mako a maimakon fam dubu £70 da take bayansa duk mako a matsayin albashi.