Dan wasa mai tsaron raga na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, dake kasar Ingila, mai suna Hugo Lloris, zai tafi jinya ta tsawon makwanni biyu.
Hugo Lloris, dan kasar Faransa ya samu rauni ne bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a wasan da suka yi da takwararta na Real Madrid, na gasar cin kofin zakarun Turai (UCL) na bana ranar laraba 1/11/2017 inda Tottenham ta doke Real Madrid da ci 3-1, ita kuma Hugo Lloris, suka yi karo da Sergio Ramos, na Real Madrid.
Amman duk da wannan rauni sai da Hugo, yaci gaba da kama wasan har zuwa tashi.
Don haka ana ganin dan wasan bazai samu damar kama wasannin da kasarsa Faransa, zata yi tsakaninta da kasar Wales da kuma kasar Jamus ba a ranar 10/11/2017.
Tuni dai kocin kasar Farans,a Didier Deschamps, ya cire sunan Hugo Lloris, a cikin jerin sunayen 'yan wasan da zasu fafata masa a wasannin.
Facebook Forum