Matsalar fyade babban matsalar ce da take addabar jama’a shi yasa na yi fim din Kanjamau wato cutar HIV duba da yawaitar fyade da ke aukuwa a cikin alumma.
Yadda matsalar fyade ke kara ta’azara yake kuma kawo damuwa da matsaloli ga zamantakewa musammam ma ga kananan yara da matasa.
Ali Rissini darakta a masana’antar Kannywood, mai shirya fina finai kuma jurumi a masana’antar , ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir, a Kano.
Ya kara da cewa ya dauke fim din Kanjamau ne domin ya fadakar da alumma ilolilin da ke tattare da harka ta fyade, tare da cewa mafi yawan fina-finansa suna duba ne da matsalolin da ke adabar alumma a yanzu.
Ali Rissini ya ce a fim dinsa na Sani Makaho yayi duba ne akan iyaye da suke mara yaran wajen aiwatar da badala, inda a fim din yake nusar da iyayen da suke barin ‘yayansu shagala a duniya domin samun abin duniya .
Haka nan a fim din almajira inda ya waiwayi masu yin karya da cewar su ‘yan gudun hijira ne domin su sami sadaka ko taimako.
Ali ya ce a lokuta da dama yana lura da matsalar da ake fuskanta a lokacin ne sannan ya fitar da fim domin wa’azantarwa akan batun.
Facebook Forum