‘Yan Nijer mazauna kasashen waje kimanin 103164 daga cikin 205314 da suka yi rajista ne suka halarci runhuna a zaben 18 ga watan Yunin 2023 da nufin tantance mutanen da za su wakilce su a majalisar dokokin kasa inji shugaban hukumar zabe ta CENI a yayin kwarya kwaryan bukin da aka shirya a wannan Laraba a dakin taro na 'Palais des Congres' da ke birnin Yamai.
Me Issaka Sounna ya kara da cewa daga cikin kujeru 5 da aka yi zawarcinsu jam’iyyar MNSD NASARA ta sami kujera 1 sannan PNDS TARAYYA ta lashe kujeru 2, sai kuma MODEN LUMANA wadda ta sami kujeru 2.
Jam’iyyar MODEN LUMANA wace ta fafata a zaben na 18 ga watan Yuni cikin yanayin rarrabuwar kawuna na alfahari da yadda ‘ya'yanta suka jajirce har aka kai ga samun abin da wani kusanta Mahamadou Maidouka ke kira galaba.
A shekarar 2016 ne ‘yan Nijar mazauna ketare suka fara aiko da wakilai a majalissar dokokin kasa, a wancan lokaci daga cikin kujeru 5 PNDS TARAYYA na da 3. Ganin yadda a wannan karon ta tashi da kujeru 2, wasu na ganin abin tamkar wata manuniya ce ga jam’iyyar mai mulki. To amma Boubacar Sabo na alakanta lamarin da tsarin fasalin zabe.
Jam’iyyu 10 ne suka fafata a wannan zabe da ke matsayin na cike gurbin kujeru 5 na majalisar dokokin kasar mai kujeru 171 a bisa ka’ida ‘yan Nijar mazauna ketare kan kada kuri’unsu ne lokaci guda da sauran jama’ar cikin gida. To sai dai annobar coronar da aka fuskanta a 2020 ta tilasta dage zaben na ‘yan diasfora. Yanzu dai kallo ya koma wajen kotun tsarin mulkin kasa wace ke da hurumin tabbatar da sahihancin sakamakon zaben wato ko ta yi na’am da shi ko akasin haka.
Saurari rahoton cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5