An Yi Jana'izar Wasu Sojojin Saman Najeriya Da Suka Mutu A Fagen Daga

Gawar Sojojin Saman Najeriya

Rundunar sojojin saman Najeriya tayi jana'izar dakarunta da suka rasu a hadarin jirgin yakin nan na Mi-35, dake rufawa dakarun bataliya ta 145 baya a Damasak dake yakar yan Boko Haram.

Jana'izar da aka yi a makabartar sojoji dake Abuja, ta ja hankalin mahukunta, sojoji da sauran 'yaan Najeriya.

Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar sojojin saman Najeriya Air Marshall Sadique Abubakar ya ce sojojin saman za suyi iya bakin kokarinsu don gaggauta kawo karshen wannan yaki.

Yana mai cewa hakan zai sa wadannan dakaru basu rasa rayukansu haka kurum ba, ya kuma jaddada cewa wannan yaki waat gwagwarmaya ce ta kasar Najeriya baki daya.

Babban hafsan dake kula da harkokin mulki a hedkwatar sojin saman, Air Vice Marshall Kingsley Lar yace baki dayan wa'yannan sojoji sun taka rawa sosai wajen ragargaza ‘yan Boko Haram a shiyyar arewa maso gabas.

An dai yi jana'izar sojojin wadanda aka lullubesu cikin tutar Najeriya bayan wani faretin soji da harba bindigogi sama don karrsmasu a gaban ministan tsaron kasar Mansur Dan Ali da babban Hafsan Hafsoshin Rundunar Tsaron Najeriya Janaral Abayomi Gabriel Olanishakin.

Ga rahoton Hassan Maina kaina daga wurin jana’izar a Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

An Yi Jana'izar Wasu Sojojin Saman najeriya