Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bai Kamata A Sake Zaben Gwamnonin Da Basu Yi Aiki Ba-Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar
Shugaba Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce bai kamata talakawa su sake zaben gwamnonin da basu yi masu aiki ba, da ya hada da gaza biyan albashin ma’aikata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dake neman wa’adin mulki na biyu karkashin tutar Jam’iya mai mulki APC ya bayyana cewa, ya kamata masu kada kuri’a su zabi ‘yan takara bisa cancanta da kuma aikin da suka yiwa talakawa,

A cikin hirarshi da Sashen Hausa, shugaba Buhari yace bai ga dalilin da zai sa gwamnatin tarayya ta ba gwamnoni kudi domin gudanar da ayyuka amma su gaza biyan albashi ba. Yace yana mamakin yadda gwamnoni zasu iya zuwa su kwanta su yi barci bayan sun san akwai mutanen dake aikin gwamnatin basu biya su albashinsu ba, sanin suna da gidaje, suna da iyali, basu biya kudin haya ba, basu biya bukatun iyalansu ba, da suka hada da biyan kudin makaranta, da zuwa asibiti da sayen abinci.

Shugaba Buhari yace tsarin dokar kasar ya ba gwamnonin ‘yancin kashe kudin da suka samu ba tare da tsangwama ba, sai dai wannan ya zama damar da wadansu suke fakewa suna kin yiwa al’umma aiki. Sabili da haka ya shawarci talakawa su yi amfani da ‘yancinsu na zabe su zabi wadanda suka san zasu yi masu aiki.

Dangane da batun yaki da cin hanci da rashawa, shugaba Buhari yace hanyar da yake bi a halin yanzu ita ce hanyar da tsarin damokaradiya ya yarda da shi. Yace a baya ya dauki wani mataki na dabam, amma kasancewa yanzu ana mulkin damokaradiya ne tilas yabi tsarin. Sai dai yace duk da yake tsarin yana daukar lokaci, duk da haka, haka na cimma ruwa.

A nashi bayanin, dan takarar jam’iyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yace matakin farko da ya kamata gwamnati ta dauka na yaki da cin hanci da rashawa shine tabbatar da yiwa talakawa aiki da samar masu da hanyoyin dogaro ga kai da biyan bukatunsu na yau da kullum. Yace tilas ne ‘yan kasa su sami wadata ta kowacce hanya, in sana’a suke yi, in aikin gwamnati suke yi da sauransu.

Da aka tambaye shi ko yana ganin rashin kiyaye doka da oda ne yasa aka gaza shawo kan matsalar cin hanci da rashawa, sai dan takarar ‘jam’iyar PDP yace baya ganin haka, kasancewa ana kama wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa ana tukumarsu, ana kuma hukumta wadanda ake samu da laifi.

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, irin rawar da ya taka a samar da ayyukan yi, da kwarewa da yake da ita wajen kirkiro da masana’atu zai taimaka mashi wajen shawo kan matsalar rashin aikin yi musamman tsakanin matasa.

Dangane da batun canza sheka, yace shi da dan takarar jam’iyar APC, shugaba Muhammadu Buhari dukansu sun canza sheka sau da dama, wanda ‘yanci ne da kowanne dan kasa yake da shi.

Saurari wannan bangaren hirar da Aliyu Mustapha ya yi da ‘yan takarar manyan jam’iyun siyasar Najeriya, Shugaba mai ci, Janar Muhammadu Buhari na jam’iyar APC, da kuma dan takarar babban jam’iyar hamayya PDP tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa.

Hira da Shugaba Buhari da Atiku Abubakar-PT4-12:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:11:38 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG