Wasu motocin kawa, da na alfarma da aka kwace daga wajen dan shugaban kasar Equatorial Guinea an yi gwanjonsu akan kudi sama da dalar Amurka miliyan 23.
Hukumomin kasar Switzerland sun kwace motocin guda 25 bayan da aka yi binciki akan batun halasta kudaden haram.
Wadannan motoci mallakin Teodoro Nguema Obiang Mangue, wanda shi ne mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea da ya shafe shekaru 40 akan karagar mulki, shugaba Theodora Obiang.
A cikin motocin da aka sayar a jiya Lahadi akwai Lamborghinis, Ferraris, Bentleys, Rolls Royces da kuma McLaren.
Farar Lamborghini Veneno Roadster da ba kasafai ake samunta ba, daya ce daga cikin guda tara kawai kuma wadda harsashi baya huda ta, da aka sayar da ita akan dalar Amurka miliyan 8 da digo 3 da wanda ya saya baya so a bayyana sunansa.