Kwamitin Majalisar Dokokin Jamhuriyyar Nijar mai kula da sha’anin doka ya gabatar da rahotonsa, bayan gudanar da wani zagaye a jihohin Yamai da Dosso da nufin fadakar da al’umma akan mahimmancin zaman lafiya a wannan lokaci da ake fuskantar kananan fitintinu a can da nan.
Jin ta bakin jama’a a dangane da matsalolin da suka fi ci masu tuwo a kwarya domin yi wa tufkar hanci shi ne makasudin zagayen da kwamitin kula da sha’anin doka a majalisar dokoki ya gudanar a jihohin Dosso da Yamai, da nufin inganta matakan zaman lafiya ta hanyar inganta rayuwar ‘yan kasa kamar yadda kakakin wannan kwamitin, dan majalisa Lawali Moussa, yayi Karin bayani a yayin gabatar da rahoton karshen ziyara.
Fannin shari’a na daga cikin batutuwan da talakkawa suka nuna bukatar ganin an yiwa gyara, domin kawarda dukkan wani mugun tunani daga kawunan jama’a, mafari kenan da mambobin wannan kwamiti suka ziyarci ofishin ministan shari’a da dangoginsa, lamarin da ya bada damar jin ta bakin ma’aikata.
Yanayin tsaro a yankin Sahel wani al’amari ne da kusan a kowane rana ke bijirowa da salo kala-kala, saboda haka samun hadin kan jama’a a yakin da kasashe suka kaddamar da kungiyoyin masu tayarda kayar baya wani mataki ne da ka iya dakile dukkan wata tashin-tashina, a cewar Dan majalisa Chitou Maman, mamba a kwamitin CAJI.
A shekarar da ta gabata ne majalisar dokokin Jamhuriyar Nijer ta yanke shawarar aikawa da tawagogi akai-akai zuwa sassa daban-daban, domin jin koke-koken ‘yan kasa a hukunce a matsayin wani riga kafin kaucewa barkewar rigingimu masu nasaba da tabarbarewar yanayin rayuwa.
Ga cikakken rahoton Wakilin muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum