Ya kuma kara bayyana cewa ya zuwa wunin wannan Laraba ba su san inda aka dosa da shi ba ballantana abin da ake zarginsa da aikatawa ba.
A cewarsa "wadanda suka yi wannan aika-aika sun tafi da wayarsa da komfuta da akwatinsa duk kuwa da cewa ba su gabatar da wata takardar shaidar samun izinin yin haka a hukunce ba’’.
Moussa Tchangari dai a makon jiya ya halarci taron kungiyoyin agaji na kasashen Afirka a birnin Abdijan kafin ya sauka Abuja inda kungiyar CDD ta shirya taro.
Kungiyar kare hakkin 'dan adam ta Roddadh a sanarwar da shugabanta Tsayabou Laouan Salao ya saka wa hannu ta bayyana takaici kan faruwar wannan al’amari da ta ce ya saba wa doka.
Saboda haka kungiyar ta yi kiran hukumomi su yi wa jama’a bayani game da lamarin.
Duk da cewa Nijar na karkashin mulkin soja babban magatakardan kungiyar Alternative Moussa Tchangari na daga cikin 'dai'daikun ‘yan farar hular kasar da ke kara jaddada matsayinsu na ‘yan rajin kare dimokradiyya, saboda abin da ya kira mulki mafi bai wa talaka walwala da hanyoyin ci gaban al’umma.
A watannin da suka gabata wata ‘yar jarida Samira Sabou mai sukar gwamnatin CNSP a kafafen zamani ta fuskanci makamancin wannan al’amari inda wasu jami’ai suka dira gidanta suka yi awon gaba da ita kafin a ji duriyarta a ofishin ‘yan sandan farin kaya bayan makwanni.