Wani Alkali a Rasha ya yankewa shugaban ‘yan adawa Alexei Navalny hukuncin je-ka-gyara-halinka na tsawon shekaru biyar, bayan da aka same shi da laifin yin almubazzaranci.
WASHINGTON D.C. —
Ana kuma tunanin hukuncin zai iya hana shi tsayawa takarar neman shugabancin kasar.
Sai dai Navalny ya ce zai kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara, sannan zai kalubalanci shugaba Vladimir Putin, idan har ya nemi a sake zabensa a matsayin shugaban kasa.
Dokar Rasha dai ta haramtawa duk wanda aka samu da aikata wani babban laifi, da ya hada da almubazzaranci tsayawa takarar wani mukami har na tsawon shekaru 10.
Navalny ya fara samun karbuwa a Rasha, tun bayan da ya fallasa almundahanar dake faruwa a ma’aikatun gwamnati.
Shi ne kuma ya jagoranci zanga zangar da aka yi a shekarun 2011 da kuma 2012 da aka gudanar domin nuna adawa a lokacin da Putin zai dawo neman mulkin shugabancin kasar ta Rasha.