Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Ta Dakatar da Taron Manema Labarai Na Kullum


Rex Tillerson Sakataren Harkokin Wajen Amurka
Rex Tillerson Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ba za ta kira taron manema labarai na kullum ba a wannan makon, wani sabon al'amarin da ake gani tun bayan rantsar da Shugaba Donald Trump.

Mai magana da da yawun Ma'aikatar, Mark Toner, ya gaya ma Muryar Amurka cewa Ma'aikatar za ta cigaba da amsa tambayoyin manema labarai, saidai kawai ba za ta zauna da 'yan jarida irin na kullum ba a wannan mako, wato tun daga 6 zuwa 10 ga wata. Ya ce to amma jami'an da abin ya shafa za su maido da hira da 'yan jarida na kullum da zarar sun samu sukunin hakan.

Rabon a kira taron manema labarai na kullum a Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka tun ran 19 ga watan Janairu, lokacin da kakakin Ma'aikatar, John Kirby, wanda nadin siyasa ne kuma tsohon sojan ruwa, ya yi jawabinsa na karshe.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG