Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ba Ta Ji Dadin Kalaman Batanci Kan Putin Ba


Fadar Kremin ta Rasha ta nemi dan jaridar gidan talbijin na Fox News Bill O’Reilly da ya ba da hakuri bisa wasu kalamai da ya yi na batanci kan shugaba Vladimir Putin, yayin da yake hira da shugaban Amurka Donald Trump.

A hirar, OReilly ya kira Putin a matsayin “Mai Kisa” bayan da Trump ya ce ya na girmama shugaban na Rasha.

Kakakin Fadar ta Kremlin Dmitry Peskov ya ce ba za su lamunci irin wadannan kalamai da suka fito daga bakin dan jaridar ba, wadanda ya kwatanta a matsayin na cin-fuska ne.

A lokacin da O’Rielly ya tambayi shugaba Trump, me ya sa ya ke girmama Putin duk da cewa ya san tarihinsa kan irin munanan ayyukan da ya yi a baya, sai Trump ya ce mai “akwai masu kisa da dama, kuma Amurka ma ba za ta iya wanke kanta daga ciki ba.”

Wadannan kalamai na Trump dai sun sa wasu daga cikin ‘ya jam’iyarsa ta Republican cikin damuwa, inda Shugaban masu rinajye Mitch McConnel ya ce Putin ya yiwa Amurka zarra wajen aikata manyan laifuka, domin shi Putin tsohon “dan dabar” hukumar leken asiri ta KGB ne.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG