An sami mutanen uku ne da laifin hada baki su yaudari wani matashi dan shekara 21 da ke kasuwanci a Lagos, suka kai shi wani asibitin kula da masu cutar koda a London da nufin a cire kodarshi a dasawa ‘yar Ekweremadu mai suna Sonia, da ke fama da ciwon koda.
An yankewa Ekweremadu hukumcin daurin shekaru 9 da watanni 8 a gidan yari sabili da rawar da ya taka a wannan yunkurin, bayan da kotun ta ce, sun yi wa matashin alkawarin ba shi tukuicin kudi fan dubu 7, kimanin Naira Miliyan 4 kudin Najeriya, da kuma yi mashi alkawarin zama ya ci gaba da aiki a Ingila.
Kotun har wa yau ta yanke wa Beatrice Ekweremadu hukuncin daurin shekaru hudu da watanni shida, inda ake bukatar tayi akalla rabin wa’adin a gidan yari. Obeta, wanda ya taimaka wajen shirya wurin girbin gabobi bayan da shi kansa, ya samu dashen koda a wata cibiya da ake dashen koda, Royal Free, a watan Yulin 2021, daga wani mutum da ake zargi da safarar su daga Najeriya, an yanke masa hukuncin daurin shekaru 10. Dole ne ya kasance a gidan yari na tsawon kashi biyu bisa uku na tsawon daurin.
Masu taimakawa alkali yanke hukumci sun sami mutanen uku da laifi ne, a watan Maris a wata tuhuma irinta ta farko karkashin dokar haramta fataucin gabobin dan'adam ta dokar haramta bautar zamani.
Da yake yanke hukumci, Alkali Jerery Johnson ya bayyana cewa, tsohon mataimakin Shugaban Majalisar Dattijan, Ike Ekweremadu, ya kasance dan Majalisa lokacin da Majalisar Tarayyar Najeriya ta kafa dokar nufin haramta fataucin gabobin bil adama.
Binciken kotun ya gano cewa, Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijan ya ba wadansu ma’aikatan asibitin Royal da ke Ingila cin hanci domin su gudanar da aikin dashen kodar, amma hukumomin asibitin su ka ki amincewa da yunkurin dashen da Ekweremadun ya yi a watan Maris din 2022. An gano makircin ne a lokacin da mutumin ya je wurin ‘yan sanda a watan Mayu domin ceton ransa saboda imanin ya cewa ko ya koma Najeriya, za a cire kodarshi da yake wannan yunkurin bai cimma nasara ba a Ingila.
Rahotanni na nuni da cewa, Majalisar dattawan Najeriya da Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka sun bukaci alkalin ya tausaya wa Ekweremadu, wanda abokin kawancen tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne a siyasance.
A cikin wata sanarwa da 'yan sanda suka fitar bayan yanke hukuncin, mai gabatar da kara Joanne Jakymec ya soki wadanda ake tuhumar sabili da watsi da bukatar walwala, da lafiyar wanda aka azabtar, da kuma yin amfani da matsayinsu don cimma burinsu.
A yayin shari’ar, matashin ya ce yayi tsamnain cewa, an kawo shi Birtaniya ne don yin aiki. Bai san ainihin dalilin kawo shi Ingila ba sai a gaban likitocin asibitin Burtaniya ne aka gaya mashi cewa, za a cire gabar jikin shi ne.
Ku Duba Wannan Ma Majalisar Wakilan Najeriya Za Ta Tuntubi Birtaniya Kan Ekweremadu