Barayin dabbobi da masu satar mutane da 'yan fashi sunyi shekaru suna addabar al’ummar wannan yankunana tare da tauye musu zaman lafiya.
Duk da yake an jinjina tare da yaba irin tsare tsaren da za ayi amfani da shi wajen samun nasarar wannan yaki da ta’addanci a yankin Zamfara da makwabtan jihohi. Sai dai wasu mutane na nuna damuwarsu kan cewa ba a hada da sarakunan gargajiya ba da ‘yan kungiyoyin banga da na tauri cikin tsare tsaren don samun nasarar yakin.
A cewar sanata Sa’idu Mohammed Dan Sadau, mutanen Zamfara musammanma na yankin Dan Sadau sun gani a kasa, domin irin kayan aikin da aka girke don tabbatar da an samar da zaman lafiya.
Saurari cikakken rahotan Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5