Alkalin kotun Muhammad Idris shi ya zartas da hukumcin kan karar da wani lauya mai fafutikar kare hakin bil Adam, Mr. Tolu Ani Adebiyi, ya shigar.
Mr. Adebiyi ya kalubali karin kashi 45 cikin dari da hukumar samar da wutar lantarki ta yi a farkon wannan shekarar.
Hukumcin ya umurci hukumar samarda wutar lantarki da sauran kamfanoni dake karkashinta da su koma tsohon farashin tare da gargadin gwamnatin tarayya ta bi umurnin kotun.
Alkalin ya bayyana cewa hukumar samar da wutar lantarki ta kasa ta karya sashe na talatin da daya da talatin da biyu da kuma saba'in da shida na dokar da ta kafa hukumar. Yace hukumar tayi gaban kanta ne wajen kara farashin wutar lantarki ba tare da tuntuba ba kamar yadda dokarta ta bukata.
Kakakin hukumar Dr. Usman Arabi ya shaidawa Muryar Amurka basu ga hukumcin da kotun ta zartas ba saboda haka ba zasu iya maida martani a kai ba.
Karin farashin ya jawo kace nace tsakanin hukumar da kungiyar kwadago. Yunusa Tanimu na kungiyar kwadago yace suna adawa da karin ne domin ya sabawa doka kuma ya kara jefa talakawa cikin wahala da kuncin rayuwa.
Hukumcin ya zo daidai lokacin da da 'yan majalisar kasar ke yin muhawara akan karin kudin da kuma sabon yunkurin hukumar na sake kara farashin wutar cikin wannan shekarar.
Dan majalisar wakilai Aliyu Madakin Kira ya shigar da wani kuduri wanda ya bukaci hukumar wutar lantarkin ta dakatar da karin.
Yanzu dai mutane na korafin rashin samun wutar amma duk da haka abun da suke biya ko da wuta ko babu ya ninka biyu akan na da.
Ga karin bayni.