Taken satin rigakafi na duniya na bana shine Fatan tsawon rayuwa ga kowa. Domin kokarin hada kan alumma wajen yin rigakafi, ta yadda zasu cimma burinsu wanda ake tsammanin zai taimaka wajen kare yan uwansu tare da samar da ingantacciyar rayuwa.
Haka kuma hukumar ta ware ranakun ne don ganin gwamnatoci sun bi dukkan hanyar da ta dace don samar ingantattun rigakafi ga al’umma.
Har ila yau hukumar na kokarin ganin tabbatar da cewa a’lumma a duk fadin duniya sun samu kariya daga cututtuka masu yaduwa da zummar kawar da wasu daga cikin cututtukan.
Jami'i a hukumar lafiya matakin farko ta kasa bangaren bada agajin gaggawa na al'amuran polio Dr. Usman Sa'idu Adamu yace rigakafi ya taimaka wajen kawar da cututtuka da dama a Najeriya.
A nashi bangaren Dr. Lawal Musa Tahir ya jaddada muhimmancin yin allurar rigakafi.
Bincike ya nu na cewa rigakafi kan kare miliyoyin mutane daga kamuwa da cututtuka a kowacce shekara, kuma shine matakin farko dake kare yaduwar cututtuka a tsakanin al’umma wanda yasa Hausawa kance rigakafi yafi magani.
Saurari cikakken shirin cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5