Ana ta maida wa Shugaban Amurka Donald Trump martani game da wasu kalamai da aka ce ya jefi baki 'yan cirani daga wasu kasashen da aka ce ya kirasu da kwatankwacin 'ramin masai'.
WASHINGTON DC —
Donald Trump ya bawa 'yan majalisun Amurka mamaki yayin da ake zaman tattaunawa kan maganar baki a ranar Alhamis, yayin da aka bada rahoton ya kira kasar Haiti da wasu kasashen Afirka da “Ramin Masai”.
Kamar yadda kafafen yada labarai suka rawaito ciki har da Jaridar Washington Post da New York Times da kuma gidan talbijin CNN. Shugaban yayi tambayar “Me yasa ake maganar wadannan mutanen da suka fito daga kasashen da suke kamar ramukan Masai?”
Trump yace, me yasa Amurka ba zata dinga kyale mutane masu yawa daga kasashe irinsu Norway su dinga shigowa Amurka ba, maimakon wasu mutane daban. A Larabar da ta gabata ne dai Fira Ministar kasar ta Norway ta ziyarci Amurka tare da ganawa a fadar gwamnati ta White House.