An Tura Jiragen Yaki Jihar Filato

  • VOA Hausa

jirgin yaki mai saukar angulu kirar Mi-35P

Rundunar sojin saman Najeriya ta aika da jirgin yaki mai saukar ungulu Mi-35P da kuma wani mai sa ido da kuma samar da bayanai ISR, a wani yunkurin shawo kan rikicin da ya barke a jihar Filato.

A wata sanarwar da jami’I mai hulda da jama’a na rundunar sojin ya fitar, jiragen za su taimakawa ayyukan da sojojin kasa ke yi a jihar.

Haka zalika, rundunar ‘yan sandan Najeriya ita ma ta aika da dakaru na musamman karkashin jagorancin mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda mai kula da ayyuka wanzar da zaman lafiya a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, ACP Jimoh Moshood ne ya bayyana hakan yau Litinin inda ya ce dakarun za su je aikin wanzar da zaman lafiya garin barikin-Ladi, da Riyon, da kananan hukumomin kudancin Jos inda jama’a da dama suka rasa rayukansu a karshen makon da ya wuce.

Haka kuma za su je da jirgi mai saukar ungulu guda biyu, da tankoki biyar da ‘yan sandan ko ta kwana da sauransu.

A karshen makon da ya gabata ne rikici tsakanin manoma da makiyaya a Barikin Ladi ya yi sanadin mutuwar mutane 86. Shugaba Buhari ya yi tur da asarar rayukan, da kuma zargin 'yan siyasa da rura wutar rikicin.