Lauyan gwamnatin Amurka Martin Estrada ne ya sanar da tuhumar a jiya Alhamis, yana mai cewa, likitocin sun ba Perry magani mai yawa na ketamine da har sun nuna shakkun a cikin sakon tes ko nawa tsohon tauraron wasan "Friends" zai yarda ya biya.
Estrada yace "Wadannan da ake tuhuma sun yi amfani da jarabar shan miyagun kwayoyi da Mista Perry ke fama da ita don arzuta kansu. Sun san abin da suke yi bai dace ba."
Perry ya mutu a watan Oktoba saboda yawan ketamine da aka dura masa, kuma mataimakinsa da ke zama tare da shi ya yi mashi allurai da yawa na miyagun kwayoyi a ranar da ya mutu. Mataimakin nashi, Kenneth Iwamasa, shi ne wanda ya iske Perry ya mutu a wannan rana.
Hukumomi sun bayyana cewa, jarumin ya je neman maganin wurin likitocin biyu da aka tuhuma, bayan da likitocinsa suka ki ba shi ketamine da yawa da yake so.
Shugabar Hukumar yaki da miyagun kwayoyi Anne Milgram ta ce wani lokaci, dan wasan ya biya dala 2,000 kan kwalin ketamine wanda daya likitan ya saya dala 12.
An kama biyu daga cikin mutanen, ciki har da daya daga cikin likitocin da ake tuhuma, jiya Alhamis, in ji Estrada. Biyu daga cikin wadanda ake tuhumar, ciki har da Iwamasa, sun amsa laifin da ake tuhumar su da su, kuma mutum na uku ya amince ya amsa laifin.
Daga cikin wadanda aka kama a jiya, akwai Dr. Salvador Plasencia, wanda ake tuhuma da laifuka bakwai na rarraba ketamine da kuma tuhume-tuhume biyu da suka shafi bada bayanan karya bayan mutuwar Perry.
An kuma kama Jasveen Sangha, wadda masu gabatar da kara suka bayyana a matsayin dillaliyar miyagun kwayoyi da aka fi sani da "Queen ketamine" Maganin Ketamine da Sangha ta kawo ya yi sanadiyar mutuwar Perry, in ji hukumomi.
Mai gabatar da kara ya ce wadanda ake tuhumar sun yi musayar sakonni jim kadan bayan mutuwar Perry suna nuna ketamine a matsayin sanadin mutuwarsa.
Perry ya shafe shekaru yana fama da jarabar shan miyagun kwayoyi tun daga zamanin da yake tashe a a wasan talabijin da ake kira "Friends," lokacin da ya zama daya daga cikin manyan taurarun talabijin na zamaninsa.
Mutuwar shahararrun mutane da dalilin ta’amali da miyagun kwayoyi lokutan baya ya sa hukumomi gurfanar da mutanen da suke kawo musu.
Ku Duba Wannan Ma Allah Ya Yi Wa Jaruma Daso Saratu Gidado Rasuwa