An kaiwa jami’an yankin da dama hare-hare a wani tashin hankali mai alaka da aikata manyan laifuffukan da suka addabi kasar Mexico a baya-bayan nan.
washington dc —
An harbe magajin jihar San Luiz Potosi dake tsakiyar Mexico, wanda yake mamba ne a jam’iyyar Morena mai mulkin kasar, tare da wasu mutane 3 a jiya Lahadi, a cewar hukumomin yankin.
An tsinci gawarwakin Jesus Eduardo Franco, magajin garin birnin Tancanhuitz, da wasu mutane 3 a cikin wata mota, a cewar ofishin mai gabatar da kara na jihar.
An kaiwa jami’an yankin da dama hare-hare a wani tashin hankali mai alaka da aikata manyan laifuffukan da suka addabi kasar Mexico a baya-bayan nan.
A watan da ya gabata, kafafen yada labaran yankin su ka ba da rahoton sare kan wani magajin gari, Alejandro Arcos, a kudancin jihar Guerrero, kasa da mako guda bayan da ya kama aiki tare da dora kan nasa a kan wata babbar mota