An Tsayar Da Ranar Zaben Kanannan Hukumomi A Jihar Filato

Hukumar zabe mai zaman kanta a jahar Pilato ta ayyana nanar goma ga watan gobe, wato Oktoba, don gudanar da zabe kananan hukumomi a jahar.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a jahar Filato, Mr. Fabian Ntung ya ce za a gudanar da zaben kananan hukumomi a kananan hukumomi goma sha uku, yayinda ya ce sauran kananan hukumomi hudu dake jahar an dakatadda zaben saboda matsalolin tsaro.

Kananan hukumomin da ba za a gudanar da zaben ba sun hada da Barkin Ladi, Jos ta Arewa, Jos ta Kudu da Riyom wadanda duka a shiyyar Filato ta Arewa suke. Mr Ntung ya ce za zarar sun sami amincewar hukumomin tsaro zasu shirya gudanar da zaben a kananan hukumomin.

Alhaji Jamilu Baba, wani dan siyasa a karamar hukumar Jos ta Arewa ya goyi bayan dakatadda zaben saboda a cewarsa hukumomi na da sanin masu shirin tada fitina lokacin zaben.

Shugaban al’umma a yankin Filato ta Arewa, Mr. Dachollom Dalyop Jambol ya ce gwamnati na neman tauye hakkin mutane ne ta hana su damar da suke da ita na zaben shugaban da suke so don haka ya ce gwamnati ta yi azama wajen dakile matsalolin tsaro a yankin.

Your browser doesn’t support HTML5

An Tsayar Da Ranar Zaben Kanannan Hukumomi A Jihar Pilato 3'11