A Najeriya ana ta ka-ce-na-ce dangane da rahotanni da ke cewa Ministar kudi, Kemi Adeosun ta yi murabus daga mukaminta.
Jaridun Najeriya da dama sun ruwaito majiyoyin da ba su bayyana sunayensu ba, wadanda ke cewa lallai ministar ta ajiye aikinta.
A 'yan watannin nan, Adeosun ta yi ta fuskantar matsin lamba kan ta yi murabus, bayan da bincike ya gano cewa takaradar shaidar kammala aikin yi wa kasa hidima ta NYSC da ta mallaka ta bogi ce.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani na kusa da minista Adeosun ya tabbatar da cewa ta yi murabus.
Ita ma jaridar Vanguard ta tabbatar da hakan a shafinta na intanet.
"Mun samu tabbacin cewa, ta (Adeosun) ajiye aikinta" Inji jaridar ta Vanguard.
Ko da yake jaridar har ila yau, ta ruwaito cewa, mataimakan ministar, sun musanta hakan.
Jaridar Punch ita ma ta ruwaito wasu majiyoyi da ba ta bayyana sunayensu ba, wadanda suka bayyana mata cewa, Adeosun ta yi murabus ne saboda badakalar takardar shaidar kammala aikin yi wa kasa hidima ta bogi da aka same ta da ita.
Sai dai shafin Twitter na gidan talbijin din kasa na NTA, (@NTANewsNow) ya bayyana cewa ministar na nan a kan mukaminta.
"Wasu kafafen sada zumunta, sun bayyana cewa ministar kudi Kemi Adeosun ta yi murabus, babu tabbacin wannan labari domin babu wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban kasa." Inji shafin Twitter na NTA.
Masu lura da al'amura sun ce, idan har ministar ta ajiye aikin nata kamar yadda rahotanni ke nunawa, hakan bai rasa nasaba da tsoron kada ta shafawa shugaba Buhari kashin kaji, yayin da yake neman wa'adi na biyu a zaben badi.
Facebook Forum