Hukumomin sun musanta cewar mayakan sa kaine suka kai harin, sun kuma kara da cewar baza’a samu karancin mai ba a sanadiyyar rashin aikin matata.
Fashewar tayi sanadiyar tashin gobara da tayi sanadiyyar lalacewar wasu na’urori, amma ba’a rasa rai ba.
Ministan kasuwanci na kasar Kamaru Luc Magloire Mbarga Atangan ya tabbatar da cewar ba za’a samu karancin mai ba ballantana Karin kudin sa.
Ya ce shekaru 2 da suka gabata Kasar ta taba samun kanta a cikin irin wanna halin, lokacin da aka rufe matatar har na tsawon watannin 8 don aiwatar da wasu gyare-gyare, kuma karanci Mai da aka samu bai yi wani tasiri ba. Domin kuwa sun kara yawan Man da ake shigowa da shi ba tare da kara kudin Man ba. Ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu kada su tsorata.