Wannan batun dai yasa Amurka hasarar a kalla dala miliyan 36, kuma yau shekaru 4 kenan ake kan binciken wannan batu, abin da mahukuntan na Amurka suka ce mutane kusan 200 ke cikin wannan badakalar.
Wannan bakaramin cin amanar kasa bane kuma da kuma tozarta aikin sojan ruwa, wanda manya-manyan jami’an soja ruwa suka aikata, inji babban mukaddashin mai shara’a Alana Robinson a jiya talata.
Ma’aikatar shari’ar tace Rear Admiral Bruce Loveless, daya daga cikin manyan sojojin ruwa mai kula da sashen tattara bayanan sirri dake ma’aikatar tsaron Amurka na Pentagon na cikin wadanda ake tuhuma a wannan abin fassalar, sai kuma wasu jamia’an sojan ruwa su 3 da suka yi murabus, haka kuma akwai warrant officer da kuma kwamanda guda.
Ana tuhumar wadannan jamia’an sojan ruwan da karban cin hanci da rashawa, kawo wa aikin shari’a cikas, tare da kantara karya gamasu bincike na gwamnatin tarayya.
Tuhumar da ake wa wadannan mutanen shine karban na goro daga dan kwangilar nan dake zaune a kasar Singaphore Leonard Francis wanda tuni ya amsa laifin sa, cewa ba shakka sun cuci ma’aikatar sojan ruwa miliyoyin daloli, shi dai wannan dan talikin ana masa lakabi da FAT LEONARD.