Matakin da majalisar tsaron kasar ta dauka na dakatar da duk wasu ayyukan kungiyoyin, ya shafi kungiyoyi kamar kungiyar likitoci ta "Doctors Without Borders" da kungiyar kiristocin katolika ta "Catholic Relief Services", wadanda ke bayar da taimakon kiwon lafiya a wasu kasashen da mutanensu ke matukar bukata.
Nicolas Agostini na wata kungiyar bada agaji ta MDD dake kare marasa karfi, yace wadanan kungiyoyin da aka dakatar sune ke aikin samarda aiyukkan kiyon lafiya da na ilmi da gwamnatin Burundi din bata samarwa.
Tun shekarar 2015 kasar Burundi ke fama da tashe-tashen hankalin siyasa. bayanda shugaban kasa Pirre Nkurunziza, ya sanar da kudurinsa na sake tsayawa takara a wa’adi na uku, ya kuma yi watsi da sukar da ake masa na cewa wa’adi biyu ne kawai kundin tsarin mulki ya bashi damar yi. Tun daga lokacin ne jami’an tsaro da matasan jam’iyya mai mulki, ke auna ‘yan adawa da kame da fyade da kuma azabtarwa harma da kashe su, a cewar kungiyar kungiyar kare ‘yancin dan adam ta Human Rights Watch.