Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Melania Trump Ta Tashi Zuwa Nahiyar Afirka


Melania Trump, uwargidan Shugaban Amurka ta tashi zuwa Afirka jiya Litini, a ziyararta ta farko zuwa kasashen waje, wadda ta yi ba tare da mijinta ba, tun bayan da ya zama Shugaban kasa.

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce ziyarar kasashe hudu da Melania Trump za ta yi, wadanda su ka hada da Ghana, da Malawi, da Kenya, da Masar, za ta mai da hankali ne kan, "kula da iyaye mata da kuma jarirai a asibitoci, da ilimantar da yara kanana, da al'adu da kuma tarihin kowace kasar ta Afirka, da kuma yadda Amurka ke taimakon kowacce daga cikin kasashen na Afirka a yinkurinsu na dogaro da kai.

Dama shirin Melania Trump na "Be Best," ko "kasance na nagari," wanda aka bullo da shi bara, ya ta'allaka ne kan rayuwar yara.

Ziyarar tata ta tsawon kwanaki biyar ka iya fuskantar matsala saboda take-taken mujinta da kuma kalamansa, ganin ya yi amfani da kalaman batunci kan Afirka.

To amma Joshua Meservey, wani mai nazarin manufofin Afirka a Gidauniyar Heritage Foundation, ya yi imanin cewa halin Trump ba zai yi tasiri kan ziyarar uwargidan tasa a Afirka ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG