A yayin ziyarar da ministan kiwon lafiya Dr Iliassou Idi Mainassara ke gudanarwa yanzu haka a karkarar ta Magaria dake yankin Zinder tawagar da ta hada da shugaban kungiyar kasa da kasa ta MSF SUISSE reshen Nijer aka gano cewa bayanan da Anne Pittet ta bayar a makon jiya, wanda ke cewa yara goma ne ke mutuwa a kowace rana a wannan yanki sakamakon tsanantar masassarar cizon sauro da cutar tamowa, babu kamshin gaskiya a tare da shi.
Rajistar da aka bude inda ake rubuta sunayen wadanda suka mutu, ministan ya gano cewa cikin watan da ya kare 10 suka mutu. A duk fadin jihar Magaria yara 75,00 suka kamu da cutar cizon sauro. Cikin adadin yara 123 ne suka mutu cikin watanni 9. Dalilin haka ba gaskiya ba ne a ce yara 10 ne mutuwa kullum
Kungiyar MSF wacce ke daya daga cikin kungiyoyin dake yiwa gwamnatin Nijer rakiya a fannin kiwon lafiya ta nesantar da kanta da abinda wannan jami’ar kiwon lafiya ta fada a wata bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta a makon jiya. Saboda haka gwamnatin Nijer ta bukaceta ta gaggauta ficewa daga kasar cikin sa'o'i 48 bisa dalilan da minista Dr Iliassou Idi Mainassara ya bayyanawa manema labarai.
Ya ce da suka tambayeta abun da ya sa ta yi hakan sai ta ce an ce ta yi ne amma kuma ta kasa bayyana wanda ya ce ta yin. Shi ma shugaban kungiyar MSF din ya ce ta yi ne da sunanta.
Sai dai masu kare hakkin dan adam irinsu Salissou Amadou na CCAC na ganin rashin dacewar wannan mataki. Yana mai cewa ba’a yi wa wannan jami’ar sa kai adalci ba. Ya tambaya menene nata ? Idan ta bada rahoto wani kuma ya bincika ya rubuta nashi sai a buba rahotannin biyu a ga abun da za’a tace ko a yi anfani dashi cikinsu.
Masassarar cizon sauro na daga cikin cututukan da masana suka saka a sahun gaban wadanda suka fi hallaka yara kanana a kasashe masu tasowa musamman dai a nafiyar Afirka haka kuma jamhuriyar Nijer ma ba ta tsira ba daga wannan matsala.
A sauraru rahoton Souley Barma
Facebook Forum