Masoyan Taylor Swift sun nuna rashin jin dadinsu bayan da aka soke wasannin da mawakiyar za ta yi guda uku wadanda tuni an kammala sayar tikitinsu a Austria.
Soke wasannin ya biyo bayan bayanan sirri da hukumomin tsaro suka ce sun gano wadanda ke cewa akwai a kai harin ta'addanci a birnin Vienna.
Da yawa daga cikin masoyanta sun dunguma zuwa shafukan sada zumunta don nuna rashin jin dadinsu kan soke wasannin mawakiyar ta Amurka ‘yar asalin jihar Pennsylvania.
Wasu masoyan nata sun bayyana yadda suka kwashe watanni suna shirin halartar wasannin har ma suka ware wasu kaya na musamman da za su saka a lokacin.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa da yawa daga cikin masoyan nata sun kashe dubban kudaden euro wajen yin tafiya da kama otel da kuma abinci.
Hukumomi sun ce sun kama mutum biyu masu tsatstsauran ra’ayi, inda dayansu ya amsa yin mubaya’a ga kungiyar IS mai ikirarin jihadi.