Tarihi Ya Kafu A Masarautar Kano Babu Hawan Nassarawa

Bisa ga a al’ada, duk rana ta uku bayan sallah, rana ce da ake hawan Nassarawa a jihar Kano, inda sarki ke zagaye anguwanni, ya je gidan sarkin Nassarawa sannan ya garzaya gidan gwamnati domin gaisuwar sallah karama ga gwamna.

Amma kwatsam a shekaran jiya da daddare sai aka bada sanarwar hana hawan nassarawa, domin dalili tsaron al'umma kamar yadda sanarwar ta ambata.

Akan haka ne wakiliyar DandainVOA ta zanta da matasa, don jin ko ya suka ji da wannan sanarwar ta soke hawan Nassarawa.

Ga rahoton Baraka Bashir.

Your browser doesn’t support HTML5

An Soke Hawan Nassarawa A Jihar Kano