Hukumar kula da gidajen Yari ta Amurka ta shirya dawowa da hukuncin kisa a Amurka bayan kwashe shekaru 16 ba tare da ana yi ba, inda aka shirya cikin watanni masu zuwa, za a rataye wasu masu laifi biyar da kotu ta yankewa hukuncin kisa, Ma’aikatar Shari’a ta sanar jiya Alhamis.
WASHINGTON, D.C. —
Hukumar kula da gidajen Yarin, za ta dauki salon da wasu jihohi su ke yi wajen amfani da magunguna domin sauya amfani da sinadarin allura da ake amfani da ita a baya. A cewar ma’aikatar harkokin wajen Amurka, yanzu haka an shirya kashe wasu mutane uku a watan Disamba, biyu kuma a watan Janairun Shekarar 2020. Ma’aikatar ta kara da cewa sauran kuma za a kashe su a nan gaba.
A shekarar 2003 gwamatin Amurka ta kashe wani tsohon sojin Amurka Louis Jones bayan an kama shi da laifin sacewa da kashe wani soja dan shekaru 19 . yanzhu haka akwai mutane 65 da gwamatin Amurka ta yankewa hukuncin kisa.