A yau Laraba, tsohon lauya na musamman, da ya yi bincike, kan katsalandan din da Rasha ta yi a zaben Amurka na 2016, Robert Mueller, ya fadawa majalisar dokokin Amurka cewa, binciken da ya gudanar, bai wanke shugaba Donald Trump daga zargin cewa, ya yi yunkurin hana binciken ba, duk da cewa, Trump, ya yi ikrarin hakan.
Yayin da aka fara kirga sa’o’i, a bahasin da yake bayarwa, shugaban kwamitin, da ke kula da fannin shari’a, Jerrold Nadler, ya tambayi Mueller, “shin ka wanke Shugaba Trump baki daya,” daga wannan zargi?
Sai Robert Mueller ya ce “a’a”, ya kuma kara da cewa, “sam ba a wanke shugaban daga zargin abin da ya aikata ba.”
Amma Mueller ya ce, ba za a iya tuhumar shugaba Trump da wani laifi ba, saboda wani dadadden tsari da ma’aikatar shari’ar Amurka, take da shi, wanda ya hana a tuhumi duk shugaban da yake kan mulki.
Ya kuma kara da cewa, tawagarsa, da ta yi binciken, ta kwashe shekara tana neman hadin kan Shugaba Trump, domin ya zo gaba-da-gaba, ya ba da bahasi, amma, sai kawai ya amsa wasu tambayoyi a rubuce, ya aiko mana.
Facebook Forum