Matsalar da kamfanin Samsung ya samu na wayar Galaxy Note 7 ya kaishi ga gurfana gaban kotu.
Wasu mutane da suka sayi wayoyin, wanda daga baya aka janye saboda suna kamawa da wuta suna fashewa, sunyi karar Kamfanin mai kera kayayyakin fasahar a Amurka.
Wannan shine karon farko da gungun mutanen da suka sayi wayoyin suka shigar da kara kotu, mutanen da suka mallaki wayar Note 7 suna bukatar da kamfanin ya gyara ko yayi musayar wayoyin ya kuma ‘kara tsawon kwanakin da in wayar ta sami matsala kamfanin zai gyara ko yayi musaya.
Samsung wanda ya dakatar da sarrafa wayoyin Note 7 a makon da ya gabata, ya fadawa mutanen da suka mallaki wayoyin da suyi jiran kwanaki ko makonni kafin a musanya musu wata wayar. Kafin nan, mutanen da suka ‘dauki bashin wayar daga wasu kamfanonin sadarwa suna ci gaba da biyan kudin wayar a duk wata, kasancewar ba zasu iya amfani da wayar ba, kamar yadda koken da suka kai kotu akan ofishin kamfanin Samsung dake Amurka, wanda yake a jihar New Jersey ke fada.
Yanzu haka dai an haramta daukar wayar Note 7 cikin jakankunan matafiya ta jirgin sama a Amurka, a makon da ya gabata ne akace duk matafiyin da ya yi kokarin daukar wayar Note 7 cikin jirgi za a kwace ta kuma a ci tarar sa.
Your browser doesn’t support HTML5