Bangaren ‘yan adawar kasar Venezuela suma za sun bi sahun masu yajin aiki yau Alhamis, rana ta biyu kuma ta karshe da aka kaddamar da yajin aiki a duk fadin kasar da zummar tilastawa shugaba Nicolas Maduro soke zaben dake tafe na wakilan da zasu rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar.
Miliyoyin ma’aikata sun yi zaman su a gida jiya Laraba, hakan ya sa babu motoci sosai akan hanyoyin da manya tituna, kuma an rufe masana’antu dayawa.
Wasu masu zanga-zanga sun sanya shingaye a wasu unguwarni don hana mutane zuwa wurin aiki, abinda ya janyo hargitsi tsakanin su da dakarun tsaro har mutum daya ya rasa ransa.
Shugaba Nicolas Maduro ya shirya cewa a ranar 30 ga watan nan na Yuli ne za a gudanar da zaben wakilan da zasu rubuta kundin tsarin mulki don maido da doka da oda a kasar Venezuela, bayan da mutane fiye da 100 suka rasa rayukansu a cikin tashe-tashen hankullan da suka rinka barkewa kusan kowacce rana ta Allah tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro tun daga watan Afirilu.