A duk lokutan zabe na Taraiya ko Jihohi, shugabannin addini da na al'umma kan yi fatan alheri da gujewa nuna bangaren da su ke marawa baya. Tsayawar su a matsayin shugabannin al'umma kan ba su martabar da zai hana kaskantar da darajar su ko furta mu su kalamai marar sa dadi.
Majalisar limaman birnin Abuja da ke da kananan hukumomi 6 ta yi gagarumin taro da bita ta wuni biyu don karawa limaman kwarin gwiwar tsayawa kan gaskiya da kaucewa marawa kowanne bangare baya a siyasa.
Majalisar dai ta hada da limaman masallatan Juma’a na dukkan kungiyoyin Islama da kan taru a muhimman lokuta duk shekara.
Limamin masallacin Juma’a na Asokoro karkashin ofishin jakadancin Saudiyya, Sheikh Sufyanu, shine shugaban kungiyar da ke karfafawa limamai su rike duk jama’a da amana da dora su kan gaskiya ba tare da daukar wani gefe ko fifita wani a siyasance ba.
Majalisar Limaman na samun kudin gudanarwa daga gidajen burodi kimanin biyu da ta kafa wadanda kan dau dawainiyar lamura ba tare da mika kokon bara ba.
Domin sauraron cikakken rahotan saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5