An Sauya Kwamandan Rundunar Yaki Da Boko Haram

BORNO: Rundunar Lafiya Dole

Yanzu Manjo Janar Abba Dikko shi ne sabon babban kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole da ke jagorantar yaki da Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabas a Najeriya, yayin da Brigediya Janar O A. Abdullahi da Brigediya Janar U.U Bassey za su jagoranci sashe na 2 da na 3 na rundunar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin kasar Brigediya Janar Texas Chukwu ya aikawa Muryar Amurka, ta nuna, Manjo Janar C.O. Ude yanzu shi ne sabon babban kwamandan rundunar kawancen kasashen yankin Tafkin Chadi.

Ya karbi aikin daga Manjo Janar Leo Irabor, da shi kuma aka mayar da shi hedkwatar tsaron kasar.

Wannan sauye-sauye da aka yi wa manyan janar-janar na rundunar sojojin Najeriyar ya fi shafar manyan kwamandodin da ke jagorantar yaki da mayakan Boko Haram.

Yanzu haka tambayar da akasarin ‘yan Najeriya ke yi ita ce ko wannan sauye - sauyen ka iya canza wani abu bisa yakin da ake da yan Boko Haram?

Hare-haren na Boko Haram a 'yan kwanakin na ya zafafa, lamarin da ke ci gaba da haifar da asarar rayuka.

Masanin tsaro Mallam Kabiru Adamu ya shaidawa Muryar Amurka cewa, babu abinda wannan sauyi zai canza, domin matsalar ba daga kwamandojin ba ne.

Ya kara da cewa, matsala ce da ta shafi ainihin irin tsarin da ake bi wajen tunkarar wannan yaki, yana mai cewa hadin kai tsakanin dakarun babban ginshiki ne na tabbatar da nasarar a wannan yaki.

Ya bayyana mamaki yadda mayakan Boko Haram za su yi kwamba cikin jerin motoci sama da 30 su afkawa garin Jakana da ke da nisan kasa da kilomita 40 daga birnin Maiduguri su shafe sa'o'i biyu suna aika-aika, amma jiragen yaki su gaza kai dauki akan lokaci.

Amma ga tsohon Hafsa a rundunar sojin kasar, Manjo Umar Yusuf, na ganin sauye-sauyen ka iya taimakawa fiye da yadda ake tunani, domin a dokar soji kamar yadda ya ce bai kamata a bar kwamanda ya wuce tsawon wata shida a filin daga ba

Ya kara da cewa duba da kwarewar sabbin kwamandojin "ba ko shakka haka ka iya cimma ruwa."

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja, Najeriya

Your browser doesn’t support HTML5

An Sauya Kwamandan Rundunar Yaki Da Boko Haram-3:00"