Rahotanni daga baya bayan nan sun nuna cewar an sassauta dokar ta bacin da sojoji suka kafa a garin Maiduguri, an kafa dokar ne a ranar larabar da ta gabata aka kuma kara wa'adin dokar a yau talata da safe.
An kafa dokar ne a sakamakon wasu hare haren da aka kai wanda yayi sanadiyyar raunata, da rasa rayukan mutane da ba'a fadi adadin su ba, harin ya hada da raunata wasu jami'an tsaron soji su biyu.
An sassauta dokar ne daga karfe shbiyu zuwa karfe biyar na marece, koda shike an sassauta dokar ne amma banda abeban hawa. a yanzu haka rahotanni na cewa akwai jama'a da dama a wani kauye waddanda matafiya ne amma an hana su shiga ko fita daga inda aka tsayar da su tun jiya, wasu daga cikin su ma sun tagayyara saboda rashin abinci da ruwan sha.
Mutane sun shiga mawuyacin hali sakamakon wannan doka kuma mutane da dama suna korafin cewar ya kamata gwamnati ta duba, ta sassauta masu wannan doka domin su sami kai mutane asibiti da sauran su.
Jama'ar dai na kokawa ne musamman saboda rashin lafiya da kuma hana zirgazirgar da aka hana ta abubuwan hawa wanda ya hada da shafar tattalin arziki da kasuwancin su.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5